Luis Rubiales ya yi murabus daga muƙamin shugabancin hukumar ƙwallon ƙafa ta Sifaniya, bayan ya sha suka saboda sumbatar ƴar wasan ƙasar, Jenni Hermoso lokacin wasan ƙarshe na Gasar cin Kofin Duniya na Mata.
Hermoso, mai shekara 33, ta ce sumbatar da ya yi mata bayan doke takwarorinsu na Ingila, ba da yardarta ba ne, kuma ta shigar da ƙara a ranar Talatar da ta gabata.
Rubiales ya faɗa a cikin wata sanarwa cewa ya miƙa takardar murabus ga muƙaddashin shugaban gwamnatin tarayya, Pedro Rocha inda ya ce ba zai iya ci gaba da aikinsa ba.
Ya kuma yi murabus daga muƙaminsa na mataimakin shugaban kwamitin zartarwa na UEFA.
Lamarin dai ya haifar da ce-ce-ku-ce cikin harkokin ƙwallon ƙafa na Sifaniya a makonnin baya-bayan nan, kuma ya shafi gasar cin kofin duniya da ƙasar ta lashe, lamarin da har ya kai ga gurfanar da Rubiales a gaban kotu
Rubiales dai ya yi iƙirarin cewa da yardar Hermoso, ya sumbace ta, kuma ita ma ta yi masa.


