fidelitybank

Dabbanci ne kisan Filato – Ƙungiyar Gwamnoni

Date:

Ƙungiyar gwamnoni ta yi Allah wadai da kashe-kashen da wasu mahara suka yi a garuruwan Ruwi da Manguna da Daffo da Josho da Hunti da ke ƙaramar hukumar Bokkos ta jihar Filato, inda ta bayyana kisan da na rashin hankali.

Shugaban ƙungiyar, gwamnan jihar Gombe, Muhammadu Inuwa Yahaya ne ya bayyana haka, inda ya ce harin – wanda ya ci rayukan mutane da dama tare da jikkata wasu ciki har da mata da ƙananan yara – yana bazarana ga zaman lafiya da ci gaban yankin arewacin ƙasar.

A wata sanarwa da kakakin gwamnan, Ismaila Uba Misilli ya fitar, gwamnan ya ce, “rayuwar ɗan’adam na da daraja da ta wuce a wulaƙanci,” in ji shi kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.

Gwamna Inuwa ya kuma yaba da ƙoƙarin gwamnan jihar Filato Caleb Mutfwang bisa matakan da ya ɗauka, sannan ya yi kira ga jami’an tsaro su ƙara ƙaima wajen kamo waɗanda suke da hannu a kashe-kashen.

“A matsayinmu na gwamnonin arewa, za mu cigaba da ƙoƙari domin kawo ƙarshen rikice-rikicen da suka dabaibaye yankin.”

nigerianewspaper

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Farfesa Jibril Aminu ya rasu ya na da shekaru 86

Allah ya yi wa Farfesa Jibril Aminu mai shekara...

Alhajin Najeriya ya rasu a tsayuwar Arfa

Wani Alhaji daga Najeriya ya rasu a filin Arfa...

Alhazai miliyan 1.673,230 ne ke gudanar da akin Hajji – GASTAT

Hukumar tattara alƙaluma ta Saudiyya (GASTAT) ta ce, Alhazai...

Isra’ila ta gano gawar ƴan ƙasarta

Rundunar sojin Isra'ila ta ce ta gano gawar ''yan...

Ma’aikatan wutar lantarki a Abuja sun fusata

Ma'aikatar kamfanin rarraba wutar lantarki na Abuja Electricity Distribution...

Ƴan Najeriya 147 da suka maƙale a Nijar sun dawo gida

Gwamnatin Najeriya ta tarɓi 'yan ƙasar 147 aka kwaso...

Alhazai Miliyan Ɗaya da Rabi ke tsayuwar Arfa

Dubun dubatar alhazai daga sassan duniya na hawan Arafa...

Sarkin Kano na 15 ya dakatar da yin hawan Sallah

Mai martaba Sarkin Kano na 15, Alhaji Aminu Ado...

Maniyacin jihar Kano da yake kokarin zama Alhaji ya rasu a Saudiyya

Daya daga cikin alhazan jihar Kano, Shu’aibu Jibrin, an...

Tinubu ya bayar da tallafin Biliyan Biyu da Tirela 20 na Shinkafa ga al’ummar Mokwa

Mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima ya ce, shugaban ƙasar...

Gwamna Adeleke na Osun ya gana da Tinubu

Gwamnan jihar Osun Ademola Adeleke ya kai ziyara ga...

An samu gawar mutane 7 a ambaliyar Neja

Rahotonni na cewa masu aikin ceto sun zaƙulo gawar...
X whatsapp