Kungiyar Jama’atu Nasril Islam (JNI), ta bayyana kisan da aka yi wa wata mata mai juna biyu, Harira Jubril, da ‘ya’yanta hudu a Jihar Anambra a matsayin “dabbacin.”
Wata sanarwa da JNI Sakatare Janar na kungiyar, Dr Khalid Abubakar Aliyu, ya fitar ranar Alhamis ta c,e irin wadannan kashe-kashe na mutanen da ba su ji ba ba su gani ba abin takaici ne.
“Mun gaji da irin wannan dabi’a. Kuma kamar yadda suka sha fada a sakonnin da muke fitarwa, ya kamata gwamnati ta rika daukar matakin gaggawa game da lamuran tsaro, domin kuwa wannan shi ne babban aikinta kamar yadda kundin tsarin mulkin Najeriya na 1999 ya bayyana,” a cewar sanarwar.
Ta kara da cewa “JNI tana matukar jin zafin yadda ake kashe Musulmai da ba su su ba ba su gani ba, wadanda ke gudanar da sana’o’insu na hannu.”
Mahaifin matar, Mallam Musa Wakili, ya nemi hukumomi su biya shi diyya. In ji BBC.
Kazalika mijinta, Jubril, ya ce ya yi kamar zai haukace bayan samun labarin kisan matarsa da dukka ‘ya’yansa.