Kungiyar Kiristocin ta kasa CAN, ta bayyana kisan da aka yi wa masu ibada a cocin St. Francis Catholic Church, Owo, jihar Ondo a ranar Lahadi a matsayin dabbanci da mugunta.
Rabaran Anselm Ologunwa, shugaban kungiyar CAN a jihar a wata sanarwa da ya fitar ranar Lahadi a Akure, ya yi Allah wadai da harin.
“Kisan wasu rayukan da ba su ji ba ba su gani ba da sunan ko wane irin salo ne laifi mafi girma da kowa ya kamata ya tashi ya yi Allah wadai da shi a cikin al’ummarmu.