Rundunar ‘yan sandan Anambra a ranar Laraba, ta tabbatar da cewa an fille kan wani tsohon dan majalisa a jihar, Nelson Achukwu.
Achukwu, wanda ya fito daga karamar hukumar Nnewi ta Kudu, shi ne mai gidan man Nelly Oil & Gas da ke Utuh.
Ya wakilci mazabar Nnewi ta Kudu 2 a majalisar dokokin jihar a zamanin gwamnatin tsohon gwamna Chris Ngige, wanda yanzu shine ministan kwadago da samar da ayyukan yi a Najeriya.
Ya wakilci mazabar Nnewi ta Kudu 2 a majalisar dokokin jihar a zamanin gwamnatin tsohon gwamna Chris Ngige, wanda yanzu shine ministan kwadago da samar da ayyukan yi a Najeriya.
An yanke masa kai ne bayan da aka ce iyalansa sun biya Naira miliyan 15 a matsayin kudin fansa ga ‘yan bindigar.
Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, DSP Tochukwu Ikenga, wanda ya tabbatar da faruwar lamarin, ya ce an gano gawar tsohon dan majalisar ne a ranar Talata, a tsakanin iyakar Uke da Ukpor Communities a yankin karamar hukumar.EnuguQ’