Rahotanni sun ce ‘yan bindiga sun kashe biyar tare da yin garkuwa da wasu hudu a Dogon Dawa, Layin Mahuta da Tabanni da ke karamar hukumar Birnin Gwari a jihar Kaduna.
Masu garkuwa da mutanen, a cikin mako guda, sun kuma yi awon gaba da wasu 17.
Shugaban kungiyar Birnin-Gwari Vanguard mai kula da harkokin tsaro da gudanar da mulki, Ibrahim Abubakar Nagari ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar jiya.
Ya ce: “A ranar 15 ga Maris, wasu ‘yan bindiga tare da Dogon Dawa- Zariya sun yi wa Haruna Tanko Dogon Dawa da wasu mutane biyu kisan gilla a Gabashin Birnin-Gwari.
“An yi garkuwa da wasu mutane takwas a hanya daya. A Layin Mahuta (Tabanni), wasu ‘yan bindiga sun kashe wani malamin makaranta Abdullahi Abubakar a kan hanyar Layin Lasan zuwa Tabanni a ranar 16 ga Maris.
“Yayin da a ranar 17 ga Maris, 2022, an kashe wani mutum dan shekara saba’in tare da sace mata bakwai a Layin Mahuta Tabanni. ‘Yan bindigar sun sace wasu mutane biyu a tsohuwar Tabanni.”
A yayin da ta ke yaba wa kokarin hukumomin tsaro da gwamnatin jihar Kaduna, sanarwar ta bukaci jami’an tsaro da su rinka mayar da martani a kodayaushe a kan kiraye-kirayen da ake yi a yankunan Dogon Dawa, Kuyello, Tabanni da Kutemeshi a Birnin-Gwari.
Sai dai jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar Kaduna, ASP Muhammad Jalige, bai amsa kiran da aka yi masa na tabbatar da faruwar harin ba ga manema labarai