Ibrahim Lawan mai shekaru 16 a duniya ya kashe kansa a kauyen Kuki da ke karamar hukumar Bebeji a jihar Kano.
A wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na karamar hukumar Bebeji na masarautar Rano, Nasiru Habu Faragai ya fitar, ta ce sarkin ya umarci hakimin kauyen da ya fara gudanar da bincike na gaskiya kan musabbabin mutuwar.
“Sarkin ya damu da lamarin, ya tambayi hakimin gundumar ko yaron yana shaye-shayen miyagun kwayoyi. Ya kuma tambayi mahaifin ko yana da matsalar tabin hankali ne ko kuma sun yi gada da wani, amma mahaifin ya ce ba a yi masa ba. Ya kuma ce ba ya shan kwaya,” in ji Faragai.
Ya kuma kara da cewa sarkin ya umarci hakiman karamar hukumar da su gudanar da addu’o’i masu yawa domin gujewa faruwar irin wannan lamari.
Kakakin Rundunar ’Yan sandan Jihar Kano, SP Abdullahi Haruna Kiyawa, bai amsa kiran da aka yi masa domin tabbatar da rahoton ba. In ji Daily Post.