Sanata Yahaya Abdullahi, ɗan majalisar dattawa, ya sauya sheka daga jam’iyyar APC mai mulki zuwa jam’iyyar PDP a jihar Kebbi.
Mai baiwa Abdullahi shawara kan harkokin yada labarai, Muhammad Jamil Gulma ya tabbatar da sauya shekar a ranar Talata.
“Dakta Yahaya Abdullahi a ranar Laraba da karfe 9 na safe zai bar Abuja zuwa Kebbi, ya zarce karamar hukumar Kamba don bayyana shekarsa a matsayin jam’iyyar PDP da kuma nuna sha’awarsa ta tsayawa takara,” kamar yadda jaridar Vanguard ta ruwaito.
Yahaya ya halarci zaben fidda gwani na gwamnan jihar Kebbi na jam’iyyar APC, inda aka ce bai samu kuri’u ba.