Akalla mutane bakwai da aka yi garkuwa da su daga jirgin kasan Kaduna zuwa Abuja aka sako ranar 28 ga watan Maris.
Mutanen bakwai da ‘yan ta’addan suka yi garkuwa da su sun hada da iyali guda shida da mace daya.
Tukur Mamu, Mawallafin Desert Herald da ke Kaduna, kuma mai ba da shawara kan harkokin yada labarai ga wani malamin addinin Islama, Sheikh Ahmad Gumi, ya tabbatar wa manema labarai a Kaduna.
Mutanen da aka sako sun hada da Abubakar Idris Garba, matarsa, Maryam Abubakar Bobo, da kuma babban dansu, Ibrahim Abubakar Garba, mai shekaru 10.
Sauran sun hada da Fatima Abubakar Garba (7), Imran Abubakar Garba (5), da kuma Zainab Abubakar Garba, ‘yar shekara daya da rabi kacal.
Abubakar Idris Garba, ma’aikaci ne a hukumar yi wa Majalisar Dokoki ta kasa hidima, dan tsohon shugaban mulkin soja ne na jihohin Kano da Benue.
Haka kuma an saki wata mata ‘yar shekara 60, Hajiya Aisha Hassan, wacce aka ce an sake ta ne sakamakon kalubalen rashin lafiya da ke barazana ga rayuwa da ta tabarbare a kwanan nan.