An yi garkuwa da wani babban jami’in Hukumar Raya Yankin Neja Delta (NDDC) Engr Kingsley Okorafor a kusa da gidansa da ke Umuadara Umulogho mai cin gashin kansa a Jihar Imo.
DAILY POST ta tattaro cewa, ‘yan bindigar sun yi awon gaba da shi ne da sanyin safiyar Asabar, kimanin kilomita uku daga wani shingen binciken sojoji a yankin.
Tuni dai sarkin gargajiya na yankin Eze, Patrick Uwalaka, ya tabbatar da faruwar lamarin.
Wata majiya ta kusa da iyalan ta shaidawa DAILY POST cewa, jami’in hukumar ta NDDC ya halarci bikin murnar marigayi, Eze Innocent Anyawu, basaraken gargajiya na yankin Ndihu a karamar hukumar Obowo, wanda ake shirin binne shi a yau Asabar 16 ga watan Yuli.