Wasu ‘yan bindiga da ke yin barna a yankin Kudu maso Gabashin kasar nan, sun kai hari a hedikwatar ‘yan sanda reshen Agwa da ke karamar hukumar Oguta a jihar Imo, inda suka kashe jami’ai akalla hudu.
DAILY POST ta tattaro cewa, lamarin ya afku ne a daren Juma’a lokacin da maharan suka mamaye yankin suna harbe-harbe kafin su shiga ofishin.
A cewar wata majiyar ‘yan sandan da ta tabbatar wa DAILY POST faruwar lamarin a ranar Asabar, lamarin ya haifar da tashin hankali a daukacin karamar hukumar.
Ya ce, ‘yan bindigar sun kona wasu motoci tare da lalata wasu kayayyaki masu daraja.
“An kai hari ofishin kuma mun samu labarin cewa an kashe jami’ai kusan hudu. Ba za a iya gano jimillar barnar ba a halin yanzu,” in ji shi.
Kokarin da DAILY POST ta yi na jin ta bakin rundunar ‘yan sandan jihar ya ci tura, domin jami’in hulda da jama’a, Micheal Abattam bai amsa kiran na su ba.


