A ranar Larabar ne wasu ‘yan bindiga suka kai hari kan mataimakin sufeto Janar na ‘yan sanda mai kula da shiyya ta 12, Audu Madaki, a unguwar Barde da ke Kaduna, inda suka kashe wani da ya ke gadin sa.
A cewar Talabijin ta Channels, Madaki da wani jami’in da har yanzu ba a tantance ko wanene ba sun tsallake rijiya da baya, amma sun samu raunukan harbin bindiga a kauyen Barde-Jargindi.
Suna kan hanyarsu ta zuwa taron Sufeto Janar na ‘yan sanda ta ƙasa, Usman Alkali Baba da manyan jami’an ‘yan sanda daga matakin kwamishinonin ‘yan sanda na wata-wata.
Babban abin da za a tattauna shi ne batun tsaro a kasar, wanda IGP ya ce, yana da matukar muhimmanci wajen samar da hanyar magance wadannan matsalolin tsaro a kasar.
Wani bangare na batutuwan da za a tattauna shi ne yadda ‘yan sanda ke karbar kudi da cin zarafi, da isasshen kariya ga barikokin ‘yan sanda, da dakile hare-haren kwantan bauna, da kuma laccoci kan wayewa da sanin makamar aiki.


