An ga ‘yan sanda dauke da makamai sun mamaye sakatariyar jam’iyyar Peoples Democratic Party PDP, dake jihar Abia a ranar Alhamis.
‘Yan sandan sun hana fita da shiga a sakatariyar da ke kan titin Finbars, Umuahia.
An ce suna aiki da umarni daga sama, a cewar jaridar Punch.
Sakataren yada labarai na jam’iyyar PDP na Abia, Fabian Nwankwo, ya ce, an bukaci ma’aikata da jami’an jam’iyyar da su yi hutun kwana daya a gida.