‘Yan majalisar dokokin jihar Oyo takwas da aka zaba a karkashin jam’iyyar PDP za su fice daga jam’iyyar.
An tattaro cewa, ‘yan majalisar da wasu jiga-jigan jam’iyyar a jihar Kudu maso Yamma sun kammala shirin komawa jam’iyyar All Progressives Congress (APC).
Naija News ta tuna cewa, a baya-bayan nan ne mataimakin gwamnan jihar Oyo, Rauf Olaniyan ya fice daga jam’iyyar PDP zuwa APC, bayan da suka samu sabani da gwamna Seyi Makinde.
Makinde, wanda ke neman sake tsayawa takara a 2023, ya ki ya zabi Olaniyan a matsayin abokin takararsa.
Daya daga cikin ‘yan majalisar PDP da suka fusata ya tabbatar da cewa, wasu ‘yan majalisar na shirin ficewa daga jam’iyyar mai mulki ranar Lahadi.
Ya shaida wa Vanguard cewa, shirin sauya shekar ya kasance ne, saboda an hana ‘yan majalisar dokokin jihar tikitin tsayawa takara a zaben 2023 na PDP.
A halin da ake ciki kuma, an yi Allah wadai da Shugaban Jam’iyyar PDP na kasa, Iyorchia Ayu, da dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar, Atiku Abubakar, kan kin kamfe na jam’iyyar a Ekiti.