A ranar Alhamis din nan ne aka shiga firgici a garin Ogbor- Nguru da ke karamar hukumar Aboh Mbaise a jihar Imo, yayin da wasu ‘yan bindiga da ake kyautata zaton ‘yan fashi da makami ne suka kai wa wata babbar motar banki kirar bullion hari.
Rahotanni sun ce maharan sun ci gaba da harbin motar, amma direban ya ci gaba da tafiya kamar yadda wani ganau ya bayyana.
Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, Michael Abattam, ya tabbatar da faruwar harin a wata ‘yar gajeruwar sanarwa.