Wasu ‘yan sanda biyu sun rasa rayukansu a safiyar ranar Asabar, yayin da wasu ‘yan bindiga suka kona shalkwatar ‘yan sandan da ke Umuguma a karamar hukumar Owerri ta yamma a jihar Imo.
Harin dai ya zo ne sa’o’i kadan bayan mataimakin babban sufeton ‘yan sanda mai kula da shiyya ta 9, a Umuahia, Isaac Akinmoyede ya bar jihar bayan wata ziyarar aiki ta kwana daya.
Hakan kuma ya faru ne kwanaki kadan bayan an kashe masu gadi biyu wadanda ke cikin rundunar hadin gwiwa ta tsaro a lokacin da wasu ‘yan bindiga suka kai wa motar sintiri hari a Okigwe. ‘yan bindigar da isar su sun tare hanyoyin shiga da fita ta tashar, ciki har da na kusa da hedikwatar karamar hukumar.
A cewar Daily Trust, ‘yan bindigar da isar su sun tare hanyoyin shiga da fita ta tashar, ciki har da na kusa da shelkwatar karamar hukumar.
Daga nan ne suka kaddamar da harin a tashar ta hanyar jefa abun fashewa da aka inganta a cikin gine-gine, bayan sun kona ofishin, sun jira su far wa jami’an da suka gudu domin tsira da rayukansu.
Wani ganau ya ce, ‘yan sandan biyu, abin takaici, sun yi taho mu gama da ruwan harsasai. An bayyana sunayensu da kamar Ifeanyi da Iyke. An ce sun yi karatun digiri na farko a Jami’ar Jihar Imo, Owerri.
Sai dai kakakin ‘yan sandan jihar, Micheal Abattam, bai samu damar bayar da amsa ba a kan harin.