Wasu ‘yan bindiga da ake zargin masu garkuwa da mutane ne sun harbe wani tsohon shugaban jam’iyyar PDP reshen karamar hukumar OrukAnam a jihar Akwa Ibom, Sir Sylvester. J Ntefre.
An bayyana cewa, an kashe jigon na PDP ne da misalin karfe 8 na safiyar Lahadi a gidansa da ke unguwar Ekparakwa bayan sun yi awon gaba da shi zuwa wani daji da ke kusa.
Maharan sun zo ne a cikin wata bakar motar Jeep, inda suka rika harbin iska don tsoratar da makwabta.
Harbin bindigar ya jawo hankalin matasan da suka daga karar suka fara bin barayin, in ji wadanda lamarin ya faru.
Kakakin rundunar ‘yan sandan Akwa Ibom, SP Odiko Mcdon, ya ce, bai samu rahoton faruwar lamarin a hukumance ba, amma ya yi alkawarin mayar da martani da zarar an sanar da hukumar.