A ci gaba da kokarin ganin an samu sauyi a cikin mintuna na karshe, za a jigilar kashin farko na maniyyata 400 daga jihar Kano zuwa kasar Saudiyya don gudanar da aikin hajjin 2022 a ranar Litinin mai zuwa.
Babban Sakataren Hukumar Jin Dadin Alhazai ta Jihar Kano, Alhaji Abba Danbatta ne ya bayyana haka ga Aminiya a Kano.
Ya ce, “Idan duk shirye-shiryen suka tafi yadda aka tsara, a yau (Litinin) za a jigilar alhazan Kano zuwa kasar Saudiyya ta jirgin Azman Air, tuni alhazan suka shirya suna jiran a kai su kasa mai tsarki.
“Kamar yadda kuke gani, tuni alhazai sun je sansanin Hajji; Jami’an mu suna gudanar da gwajinsu na karshe da gwajin COVID-19, wanda ya zama tilas kafin tashin jirgin.”
Danbatta ya bada tabbacin hukumar za ta fara jigilar jiragen.