Mazauna yankin Shanono da ke yankin Rigasa a karamar hukumar Igabi a jihar Kaduna sun sake gano wata na’urar fashewa a ranar Juma’a.
An gano na’urar sa’o’i 24, bayan an gano wani IED da aka boye a cikin bokiti a cikin al’umma.
Na’urar, wacce aka gano a ranar Alhamis, rundunar da ke yaki da bama-bamai ta jihar ce ta kwance ba tare da kuma a samu asarar rai ba.
Wani mazaunin garin, Tijjani Umar, ya ce, yara a unguwar sun gano abin da aka ajiye ranar Juma’a a cikin jarkoki da aka lullube su.
Ya ce an sanya shi kusa da rafi a cikin al’umma.
“An ajiye shi a daidai wurin da aka gano IED din ranar Alhamis. Ba mu san abin da ke faruwa a cikin wannan al’umma ba. Matar dattijona ce, ta yi gaggawar sanar da ni cewa yaran sun sake samun wani bam a cikin Jarka,” inji shi.
Kakakin Rundunar ’Yan sandan Jihar, ASP Mohammed Jalige, ya tabbatar da gano lamarin, inda ya ce, an hada tawagar da ke yaki da bama-bamai zuwa yankin.
“An killace yankin domin kare mutanen daga samun rauni yayin da mutanen mu ke can don kwance na’urar,” inji shi.
Ya bukaci jama’a da su kara sanya ido a duk inda suke a jihar.