Akalla matasa hudu ne tsawa ta kashe a garin Ago Dada da ke karamar hukumar Akure ta Arewa a jihar Ondo.
An tattaro cewa, an kashe matasan ne a yammacin ranar Laraba a yayin da aka yi ruwan sama a kauyen.
Majiyar ta shaidawa Leadership cewa, mutuwar matasan ta haifar da zanga-zanga a kauyen a ranar Alhamis, wanda ya yi sanadin mutuwar wani dattijo tare da lalata dukiyoyi da matasan suka fusata.
A cewar majiyar, abin bakin cikin matasan shi ne, matasan hudun da tsawar ta kashe duk ba ‘yan asalin kasar ba ne.
Ya kuma kara da cewa, wadanda ba ‘yan asalin kauyen ba, wadanda suka fusata da lamarin, sun yanke shawarar kai wa ‘yan asalin kauyen hari tare da lalata musu dukiyoyin su.
Da take tabbatar da faruwar lamarin yayin da aka tuntubi jami’ar hulda da jama’a na ‘yan sanda, Misis Funmilayo Odunlami, ta tabbatar da faruwar lamarin, amma ta musanta cewa an yi zanga-zanga a kauyen.