Gwamnatin tarayya ta sanar da ware Naira biliyan 5 ga kowace jiha ta tarayya ciki har da babban birnin tarayya Abuja, domin rage tasirin cire tallafin man fetur.
Gwamnan jihar Borno, Babagana Zulum, ne ya bayyana hakan yayin wata tattaunawa da manema labarai a fadar gwamnatin jihar a Abuja ranar Alhamis bayan taron majalisar tattalin arzikin kasa (NEC).
Mataimakin shugaban kasa Kashim Shettima ne ya jagoranci taron na NEC ranar Alhamis.