A halin yanzu dai shugaba Bola Tinubu yana ganawa da shugabannin kungiyar kwadago ta Najeriya NLC da TUC a fadar gwamnati da ke Abuja.
Wannan ci gaban ya zo ne a daidai lokacin da zanga-zangar da kungiyoyin kwadago suka yi a fadin kasar nan, bayan wahalhalun da ba za su iya jurewa ba sakamakon cire tallafin man fetur.