Hajiya Yar-Sokoto Jega, shugabar mata ta jam’iyyar PDP mai wakiltar Kebbi ta tsakiya a jihar Kebbi, ta koma jam’iyyar All Progressives Congress (APC).
Jega ta bayyana haka ne a lokacin da ta ke jawabi a wajen wani biki a Birnin Kebbi a ranar Laraba.
A cewarta, ta bar jam’iyyar ne saboda rashin adalci da kuma rashin shugabanci na gari.
Jega ta bayyana cewa ta yanke shawarar komawa jam’iyyar APC ne saboda dimbin nasarorin da Gwamna Atiku Bagudu ya samu, inda ta kara da cewa ta koma jam’iyyar ne da magoya baya sama da 800.
“Na shafe shekaru da yawa a PDP, ba su da wani abin da za su nunawa mutane kuma jam’iyyar ta yi watsi da mu.
“Ni ma ina amfani da kudina wajen tafiyar da jam’iyya, amma duk da haka ban ga wani sauyi da jama’ata ba, musamman matan da nake wakilta.
“Kafin sauya sheka na, ina shugabancin kananan hukumomi takwas a karkashin jam’iyyar PDP, na tafi tare da mafi yawan mabiyana,” in ji Jega.
Wasu daga cikin manyan baki da suka halarci bikin sun hada da Alhaji Abubakar Kana-Zuru, shugaban jam’iyyar APC na jihar; Alhaji Sani Zauro, shugaban kungiyar dattawan APC na jiha; da Alhaji Faruk Musa-Yaro, Mataimakin Gwamnan Jihar.