Shugaban jam’iyyar PDP reshen jihar Ondo, Fatai Adams ya rasu.
Rahotanni sun ce shugaban jam’iyyar ya rasu ne da sanyin safiyar Laraba.
Mista Kennedy Peretei, Sakataren Yada Labarai na PDP na Ondo, ya tabbatar da faruwar lamarin a safiyar Laraba.
Ya ce nan ba da jimawa ba jam’iyyar za ta yi magana da manema labarai a hukumance kan lamarin.