Kamfanin zirga-zirgar jirgin ƙasa a Ukraine ya ce, mutum fiye da 30 aka kashe tare da jikkata wasu sama da 100 a harin makamin roka da aka kai kan tashar jirgin ƙasa ta Kramatorsk.
Kramatorsk na ɗaya daga cikin tashoshin da suka rage da ke aiki a ƙasar, kuma gwamnan yankin Donetsk ya ce akwai dubban mutane a tashar yayin harin da ke yunƙurin hawa jirgi don tserewa daga yankin.
Shugaban hukumar sufurin jirgin ƙasa na Ukaraine ya ce makaman roka biyu ne suka sauka a tashar.
Tashar Kramatorsk ta shahara a matsayin ɗaya daga cikin mafiya girman wuraren ɓuya a gabashin Ukraine.