Hukumar zaben ƙasar Kenya ta sanar da William Ruto a matsayin wanda ya lashe zaɓen shugaban ƙasar Kenya da kashi 50.49 na yawan ƙuri’un da aka kaɗa.
Hukumar zaɓen ta sanar da sakamakon zaben ne a ranar Litinin da yamma.
An gudanar da zaɓen ne a ranar Talatar da ta wuce 9 ga watan Agustan 2022.
Ratar da ke tsakaninsa da abokin fafatawarsa Raila Odinga ba shi da yawa, inda shi Odingan ya samu kashi 50.4 na yawan kuri’un. In ji BBC.


