Jam’iyyar PDP za ta fara zaben ‘yan takararta a zaben 2023 kamar yadda ta tsara a yau tare da gudanar da zabukan fidda gwani na ‘yan majalisar jiha da na wakilai.
Jam’iyyar za ta kuma gudanar da zaben fidda gwani na ‘yan takarar Sanata a ranar Litinin, 23 ga Mayu, 2022 yayin da takarar gwamna zai zo ranar Laraba 26, wanda za a yi zaben fidda gwani na shugaban kasa a ranar 28-29 ga Mayu.
Wannan shi ne kudurin kwamitin gudanarwa na jam’iyyar na kasa (NWC) na jam’iyyar, a yammacin jiya, wanda kuma ya tabbatar da cewa, wakilai uku ne kawai a kowace gunduma, wadanda aka zaba a gundumomin da wakilai na kasa guda daya a kowace karamar hukuma, wadanda ake zaba a kananan hukumomi.
Majalisun yanki za su cancanci kada kuri’a a matsayin wakilai a zabukan fidda gwani da na kasa na jam’iyyar da ke tafe.