Sakamakon fitowar tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar a matsayin dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar PDP, wasu masu ruwa da tsaki na jam’iyyar na neman Sanata Iyorchia Ayu, shugaban jam’iyyar na kasa ya yi murabus.
Daily Independent ta rawaito cewa, wasu masu ruwa da tsaki na jam’iyyar na yin wannan bukata ne saboda yadda jam’iyyar PDP ta yi shiyya-shiyya. Sun yi zargin cewa shugaban kasa da dan takarar shugaban kasa ba za su iya fitowa daga shiyya daya ba.
Hakazalika sun bayyana cewa a ganawar da suka yi da gwamnonin PDP wanda ya kai ga zabensa a matsayin shugaban kasa, Ayu ya sanya hannu kan yarjejeniyar cewa, idan dan takarar shugaban kasa ya fito daga Arewa zai yi murabus daga mukaminsa don ba da damar sabon shugaban kasa daga jam’iyyar.
Ayu ya ce a shirye ya ke ya sadaukar domin ganin jam’iyyar PDP ta samu nasara a 2023 kuma zai sauka daga mulki idan jam’iyyar ta bukaci ya yi hakan, yayin da yake zantawa da manema labarai jim kadan bayan ya zama shugaban jam’iyyar na kasa.
Wani tsohon minista daga Kudu-maso-Kudu, wanda ke jagorantar zanga-zangar neman Ayu ya yi murabus, ya ce, jam’iyyar za ta fara yunkurin ganin Ayu ya mutunta yarjejeniyar kuma ya yi murabus.