fidelitybank

Da Ɗumi-Ɗumi: Masu miƙaman siyasa su yi murabus – Gwamnan Legas

Date:

Gwamnan jihar Legas, Babajide Sanwo-Olu, ya bukaci masu rike da mukaman siyasa da ke da niyyar neman mukaman zabe a zaben 2023 da su yi murabus.

Gwamnan ya bayar da umarnin ne a ranar Juma’a ta wata takarda mai dauke da sa hannun shugaban ma’aikata na jihar Hakeem Muri-Okunola.

Takardar ta umurci duk wanda aka nada da ma’aikatan gwamnati da ke sa ido kan ofisoshin zabe da nufin shiga zaben fidda gwani na jam’iyyar da su yi murabus kafin ranar 19 ga Afrilu, 2022.

“Saboda haka, duk wanda ke neman mukaman zabe ana bukatar su sanya a cikin wasikunsu na murabus. Hakazalika, ya kamata a gabatar da wasikun murabus daga dukkan wasu nau’ikan mukamai na siyasa da ma’aikatan gwamnati kafin ranar 19 ga Afrilu 2022,”in ji sanarwar.

An kuma bukaci wadanda aka nada wadanda ke son zama wakilai a zabukan fidda gwani na jam’iyyun siyasa da su mika wa sakataren gwamnatin jihar takardar murabus dinsu.

Umarnin ya yi daidai da sashe na 84 (12) na dokar zabe.

Sashen ya nuna cewa masu rike da mukaman siyasa ba za su iya shiga harkar zabe ba sai dai in sun yi murabus.

the nation newspaper 
today

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

IGP ya ba da umarnin bincike kan bidiyon ƙorafin wani tsohon ɗansanda

Babban Sufetan ‘Yan Sandan Najeriya, Kayode Adeolu Egbetokun, ya...

Amurka za ta bayar da gudunmawar dala miliyan 30 ga ‘yan Gaza

Amurka za ta ba da tallafin dala miliyan talatin...

Iran na binciken ɓarnar da aka yi cibiyoyin nukiliyar ƙasar

Ministan harkokin waje na Iran ya amince an yi...

Japan ta zartar da hukuncin kisa a karo na farko

Japan ta zartar da hukuncin kisa a karon farko...

Sojoji na zaman makoki na kwanaki 3 bayan an kashe Jami’ai 17

Rundunar Sojin sama ta bayyana fara zaman makoki na...

‘Yan Ta’adda ba za su samu mafaka ba a Nasarawa ba – Gwamna

Gwamnan jihar Nasarawa, Abdullahi Sule ya musanta zargin da...

Sojoji sun mayar da martani kan ‘Yan ta’addan Neja

Dakarun Sojin Saman kasar nan, sun ce sun ƙaddamar...

Kotu ta yanke wa Matashin da ya kashe Budurwarsa hukuncin kisa

Kotun babban birnin jihar Nasarawa ta yanke wa wannan...

PDP ta yi watsi da matakin shugaban jam’iyyar da ya dauka

Kwamitin amintattu na jam’iyyar PDP, ya yi watsi da...

Tinubu zai sanya hannu kan sabbin dokokin haraji

Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu, zai sanya hannu kan...

‘Yan Bindiga sun kashe Sojoji a Neja

Rundunar Sojin Kasa, ta tabbatar da mutuwar wasu daga...

Kungiyoyi 110 suna bukatar mu yi musu rijista – INEC

Hukumar zaɓen Najeriya, INEC ta tabbatar da samun buƙatu...
X whatsapp