Wasu da ake zargin ‘yan ta’adda ne sun yi garkuwa da mahaifiyar dan takarar kujerar Sanatan Kano ta tsakiya a jam’iyyar APC, Abdulsalam Adlbdulkarim AA Zaura.
Shugaban karamar hukumar Ungoggo, Engr.Abdullahi Garba Ramat wanda ya tabbatar da faruwar lamarin ga Solacebase, ya ce, jami’an tsaro sun sanar da shi lamarin a hukumance.
Ya ce, an yi garkuwa da Hajiya Laure ne a gidanta da ke unguwar Rangaza a kauyen Zaura na karamar hukumar ungoggo