Jam’iyyar New Nigeria Peoples Party (NNPP) ta bayyana zabin Ladipo Johnson a matsayin mataimakin da zai rufawa Rabiu Musa Kwankwaso baya a 2023.
Johnson ya fito ne daga jihar Legas dake kudu maso yammacin Najeriya, kuma ya fito takarar kujerar gwamna.
NNPP ta bayyana hakan ne ta shafinta na Twitter @nnpphqabuja1, wanda kuma sakataren yada labaran jam’iyyar na kasa, Manjo Agbor ya tabbatar da hakan.
Jam’iyyar ta rubuta: “Hanyar zuwa 2023: Bar Ladipo Johnson shine mataimakin dan takarar shugaban kasa na babbar jam’iyyar mu.”
Johnson wanda shi ne shugaban Cibiyar Ci gaban Kasuwanci da Gudanarwa na Afirka, ya ninka a matsayin mai tsara ‘The Johnson Initiative for Positive Impact.