A ranar Alhamis ne babbar kotun tarayya da ke Abuja ta yi watsi da karar da ke neman tsige gwamna Ben Ayade daga mukaminsa na ficewa daga jam’iyyar PDP.
Su biyun dai sun bar PDP ne a shekarar 2021 suka koma APC shi da mataimakin sa,
Ba su gamsu da sauya shekar ba, jam’iyyar PDP ta garzaya kotu domin ta tsige gwamnan.
Da yake yanke hukunci a ranar Alhamis, Mai shari’a Taiwo Taiwo ya ce, an samu rikicin cikin gida a jam’iyyar adawa lokacin da Ayade ya sauya sheka.