Kocin Super Eagles Austin Eguavoen ya yi murabus daga mukaminsa sakamakon gazawar da Najeriya ta yi wajen samun tikitin shiga gasar cin kofin duniya ta 2022.
A cewar Brila FM, Eguavoen ya aika da wasikar murabus din a hukumance ga NFF.
Wannan dai na zuwa ne a lokacin da Ghana ta yi kunnen doki 1-1 da Najeriya a Abuja, bayan canjaras a wasan farko da su ka yi a Ghana.