fidelitybank

Da Ɗumi-Ɗumi: Jirgin sama ya yi hatsari tare da mutane 132 a China

Date:

Wani jirgin saman kasar China, Jetliner Eastern Airlines mai ɗauke da mutane 132, ya yi hatsari a tsaunukan yankin Guangxi da ke Kudancin China, kamar yadda CNN ta rawaito.

Hukumar kula da zirga-zirgar jiragen sama ta kasar Sin (CAAC) ta sanar da faruwar lamarin, wanda ya faru a ranar Litinin.

Jirgin kirar Boeing-737 na kan hanyarsa ne daga birnin Kunming da ke Kudu maso Yammacin kasar zuwa Guangzhou a lokacin da ya bar birnin tare da fasinjoji 123 da ma’aikata tara a cikin jirgin, in ji CAAC.

Tawagar masu aikin ceto na kan hanyar zuwa wurin da hadarin ya afku, inda ake ganin gobara a wurin, amma ba a san adadin wadanda suka mutu ba, kamar yadda kafar yada labarai ta CCTV ta kasar Sin ta ruwaito. Rahotannin farko da kafafen yada labarai na kasar suka fitar sun nuna cewa, akwai mutane 133 a cikin jirgin.

A cikin wata sanarwa da hukumar ta CAAC ta fitar ta ce, an aike da tawagar masu aikin ceto zuwa wurin da hadarin ya afku.

www.najnew

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Farfesa Jibril Aminu ya rasu ya na da shekaru 86

Allah ya yi wa Farfesa Jibril Aminu mai shekara...

Alhajin Najeriya ya rasu a tsayuwar Arfa

Wani Alhaji daga Najeriya ya rasu a filin Arfa...

Alhazai miliyan 1.673,230 ne ke gudanar da akin Hajji – GASTAT

Hukumar tattara alƙaluma ta Saudiyya (GASTAT) ta ce, Alhazai...

Isra’ila ta gano gawar ƴan ƙasarta

Rundunar sojin Isra'ila ta ce ta gano gawar ''yan...

Ma’aikatan wutar lantarki a Abuja sun fusata

Ma'aikatar kamfanin rarraba wutar lantarki na Abuja Electricity Distribution...

Ƴan Najeriya 147 da suka maƙale a Nijar sun dawo gida

Gwamnatin Najeriya ta tarɓi 'yan ƙasar 147 aka kwaso...

Alhazai Miliyan Ɗaya da Rabi ke tsayuwar Arfa

Dubun dubatar alhazai daga sassan duniya na hawan Arafa...

Sarkin Kano na 15 ya dakatar da yin hawan Sallah

Mai martaba Sarkin Kano na 15, Alhaji Aminu Ado...

Maniyacin jihar Kano da yake kokarin zama Alhaji ya rasu a Saudiyya

Daya daga cikin alhazan jihar Kano, Shu’aibu Jibrin, an...

Tinubu ya bayar da tallafin Biliyan Biyu da Tirela 20 na Shinkafa ga al’ummar Mokwa

Mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima ya ce, shugaban ƙasar...

Gwamna Adeleke na Osun ya gana da Tinubu

Gwamnan jihar Osun Ademola Adeleke ya kai ziyara ga...

An samu gawar mutane 7 a ambaliyar Neja

Rahotonni na cewa masu aikin ceto sun zaƙulo gawar...
X whatsapp