Tsohon dan majalisar wakilai kuma mamba a kwamitin gudanarwa na kungiyar goyon bayan Tinubu (TSG) a jihar Borno, Abdu Musa Msheliza, ya fice daga jam’iyyar APC mai mulki zuwa jam’iyyar adawa ta Peoples Democratic Party (PDP).
Msheliza, wanda kuma dan majalisar dokokin jihar Borno ne mai wa’adi biyu, mai wakiltar mazabar Hawul, sannan ya wakilci mazabar tarayya ta Askira Uba/Hawul a majalisar dokokin kasa.
Dan siyasar wanda tuni ya samu katin zama dan jam’iyyar PDP, ya ce: “Ni mai son adalci ne, adalci, daidaito da kuma shawarwari a duk tsarin zaben shugabanni, kuma ya kamata jama’a su tashi tsaye wajen tantance wadanda za su zaba, su zaba a matsayin shugabanninsu, ba wai wani ko wasu mutane da ke zaune a wani wuri suna zabar wadanda aka gabatar a matsayin ‘yan takara a dimokuradiyyar Najeriya na karni na 21 ba,”
Msheliza ya ce, yayin da yake bayar da dalilan ficewa daga jam’iyyar APC.


