Fitaccen jarumin fina-finan Nollywood, Sir David Osagie, wanda ya yi fice wajen taka rawar sarki a fina-finai, ya rasu sa’o’i kadan bayan yana cikin shirin fim.
A cewar Jaruma, Ibiwari Etuk, Osagie ya kammala shirin fim ne ya koma dakinsa ya kwanta amma bai farka ba.
Mutuwar ta zo da kaduwa ga mutane da yawa. Osagie Ogbeosamudia David shima marubuci ne, Furodusa kuma ƙwararre me mai Hazaka.
An haife shi a ranar 1 ga Oktoba, 1968 kuma ya bar mata da ’ya’ya.