Hukumar da ke yaƙi da cin hanci da rashawa EFCC ta kama wasu mutane da ake zargi da sayen ƙuri’u a yayin zaɓen gwamnan Ekiti.
Tun da safiyar yau dama wasu daga cikin masu jefa ƙuri’a sun ta kokawa kan yadda suka ce ake sayen ƙuri’u a wasu rumfuna zaɓe.
Wani bidiyo da gidan talabijin na Channels ya wallafa a shafinsa na Twitter ya nuna yadda jami’an EFCC suka yi dirar mikiya a wata rumfar zaɓe inda suka yi awon gaba da wasu.