fidelitybank

Da Ɗumi-Ɗumi: EFCC ta bayar da belin Obiano

Date:

Shugaban hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa, Abdulrasheed Bawa, ya bayyana cewa an bayar da belin tsohon gwamnan jihar Anambra, Willie Obiano.

Obiano, wanda ake tuhumarsa da laifin almundahanar Naira biliyan 42, ya kasance a hannun EFCC, tun ranar Alhamis lokacin da aka kama shi a filin jirgin sama na Murtala Muhammed da ke jihar Legas, a lokacin da yake yunkurin tafiya kasar Amurka.

Amma da yake zantawa da manema labarai a wajen taron shekara-shekara karo na 5 na kungiyar masu yaki da cin hanci da rashawa a Afirka ta Yamma a Abuja ranar Litinin, Bawa ya bayyana cewa hukumar na jiran ya kammala belinsa.

Da aka tambaye shi dalilin da ya sa hukumar ta tsare tsohon gwamnan a hannun ta, fiye da wa’adin da tsarin mulki ya ba ta, Bawa ya ce, “Babu wani abu na siyasa game da tsare tsohon gwamnan jihar Anambra, Wille Obiano. An bayar da belinsa.”

Shugaban EFCC bai bayyana cikakken bayanin belin ba.

uanguard news

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp