Hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) ta bankado wani shiri na wasu da ake zargin gungun masu aikata laifuka ne na kulla kawance a tsakaninsu da nufin kara kai hare-hare kan muhimman ababen more rayuwa da sauran wuraren da jama’a ke yawan zuwa, kamar wuraren ibada da shakatawa, musamman a lokutan bukukuwa da bayan bukukuwa.
Wata sanarwa mai dauke da sa hannun kakakin hukumar, Dr. Peter Afunanya, ya ja hankalin jama’a kan tsare-tsare na masu aikata laifuka da su sanya idanun su a kan duk mutanen da basu aminta da su ba.
Ya ce, makasudin wadannan miyagun mutane shi ne cimma wasu muradu na son rai tare da haifar da fargaba a tsakanin ‘yan kasa.
Kakakin ya bayyana cewa, hukumar ta gargadin da ta yi tun da farko cewa, wasu kungiyoyi da daidaikun mutane na shirin haddasa rikici a kasar nan.