Shugaban Muhammadu Buhari, ya isa Dandalin Eagles Square, domin halartar zaɓen fitar da gwani na Jam’iyyar APC.
Shugaban shi ne na ƙarshe da ya shiga dandalin, inda daga shigar shi aka rufe ƙofa aka soma taron.
Kusan duka masu neman takarar shugaban ƙasa a Jam’iyyar APC sun isa dandalin Eagle Square.
Na baya-baya da suka shiga dandalin sun haɗa da Bola Tinubu da Farfesa Yemi Osinbajo.
Waɗanda suka zo tun da farko sun haɗa da Yahaya Bello da Ahmed Sani Yarima da Rotimi Amaechi da Ahmad Lawan