Baturen ‘yan sandan shiyya na yankin Magami dake karamar hukumar Gusau a jihar Zamfara, Usman Ali, ya shaƙi iskar ‘yancinsa bayan ya shafe kwanaki biyar a tsare a hannun ƴan ta’adda.
‘Yan ta’addan sun yi garkuwa da shi a ranar Talata da daddare ne, sakamakon sabbin jami’an tsaron da aka kaddamar da su.
Gwamna Bello Matawalle, yayin da yake tabbatar da faruwar lamarin, ya godewa Allah Madaukakin Sarki, bisa rayuwar dan sandan da aka yi garkuwa da shi, yana mai yabawa “kokarin da sabbin jami’an tsaron al’umma da aka kaddamar.”
Sai dai wata majiya ta bayyanawa DAILY POST cewa, abokan DPO da ‘yan uwa sun biya kudin fansa da ba a tantance ba kafin ya samu ‘yancinsa.


