fidelitybank

Da Ɗumi-Ɗumi: An ɗaure tsohuwar shugabar da ta goyi bayan kisan kiyashin musulmai

Date:

Wata kotu a Myanmar ta yanke wa babbar jagorar siyasar kasar, Aung San Suu Kyi, hukuncin daurin shekaru biyar a gidan-yari, bisa zargin cin hanci da rashawa.

Shari’ar ta mayar da hankali kan zargin da ake yi wa matar na yin awon-gaba da zinaren da darajarsa ta kai dala dubu dari shida lokacin da tana kan mulki.

Ta yi watsi da zargin da ta bayyana a matsayin shirme.

Alkalin da ya sanar da hukuncin ne jim kadan bayan fara zaman shari’ar da aka dade ana jira.

Wannan dai ita ce shari’a ta farko da aka kammala da gwamnatin mulkin soji ta gabatar tun bayan kwace mulki.

Ba wanan ne karon farko da Suu Kyi wadda ta taba lashe lambar yabo ta Nobel ta taba zaman gida yari ba.

An yi wa Ms Suu Kyi daurin-talala a watan Fabrairun 2021 lokacin da sojoji suka kifar da gwamnatinta da aka zaba.

Wannan hukuncin na nufin za ta yi shekara 11 a gidan-yari, domin kuwa a baya an same ta da laifi kan wasu zarge-zargen.

Ms Suu Kyi da mambobi da dama na jam’iyyarta na cikin fiye da mutum 10,000 da sojojin suka kama bayan sun kwace mulki.

A baya ta goyi bayan matakin da sojojin kasar suka dauka na kisan dubban Musulmai ‘yan kabilar Rohingya a 2017 lamarin da ya tilasta wa dubban su yin hijira zuwa Bangladesh. In ji BBC.

www.legit.ng

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp