A ranar Alhamis ne jihar Kwara ta tabbatar da bullar cutar kyandar biri a jihar.
Kwamishinan lafiya na jihar, Dakta Raji Rasaki, ya roki mazauna yankin da su kara kaimi wajen kula da tsaftar mutum da na al’umma a kokarin yaki da cutar.
Rahotonni na cewa, mara lafiyar, direba ne mai shekaru 29 da haihuwa daga Gbugbu a karamar hukumar Edu ta jihar.
A cikin wata sanarwa da ma’aikatar lafiya ta fitar, “Majinyacin ya kamu da alamun zazzabi, a cikin makonni biyu da suka gabata bayan an sanya masa ido.”
Sai dai a wata tattaunawa da Aminiya ta wayar tarho, Rasaki ya ce, matar mamacin da wasu makwabta hudu masu irin wannan alamari da suka yi mu’amala da shi sun killace su a hannun jami’an lafiya.