A ranar Talata ne gwamnatin jihar Gombe, ta ayyana bullar cutar kyandar Biri a jihar, bayan wasu mutane uku da ake zargin sun kamu da cutar sun dawo lafiya.
Kwamishinan lafiya na jihar, Dr Habu Dahiru, wanda ya bayyana hakan ga manema labarai, ya ce, daga cikin mutane 19 da ake zargin sun kamu da cutar ne da aka kai ma’aikatar lafiya ta jihar, an gano samfura uku na dauke da cutar.
“Mutane guda uku da aka gabatar mana suna fama da zazzabi wanda ya dauki sama da mako guda duk da maganin da ke haifar da zazzabi. Haka kuma sun samu rabe-rabe a fuska da sauran sassan jikinsu wanda hakan ya sa ake zargin cutar kyandar biri,” inji shi.
Ya kara da cewa, “Bisa la’akari da abubuwan da suka faru a sama, na sanar da bullar cutar kyandar biri a jihar Gombe.”
KARANTA WANNAN: Cutar ƙyandar Biri na bazuwa ta hanyar jima’i – Birtaniya
Dahiru, ya ce, dukkan mutane ukun da aka tabbatar sun kamu da cutar tun daga lokacin an yi musu magani kuma an sallame su daga asibiti.
Ya ce, ma’aikatar za ta yi cikakken alhakin sa ido da amsa mai inganci da nufin shawo kan barkewar cutar.
Kwamishinan ya bayyana cewa, cutar kyandar biri, cuta ce ta zonotic da ba kasafai ake samun kamuwa da ita ba tare da daukar tsawon kwanaki 5-21, wanda ke da alamomi biyu da suka hada da zazzabi, ciwon kai, ciwon jiki da rauni.
Ya ambaci wasu alamomin da suka hada da; kumburin jiki wanda ke farawa daga fuska sannan daga baya ya bazu zuwa wani bangare na jiki, gami da tafin hannu da tafin kafa.


