Hukumar shirya jarabawar kammala sakandire ta Afrika ta Yamma (WAEC), ta fitar da sakamakon ƴan makarantar da suka zana jarrabawar kammala sakandare ta yammacin Afirka ta 2022 (WASSCE).
Da yake jawabi ga manema labarai a ranar Litinin, shugaban ofishin WAEC na kasa, Patrick Areghan, ya ce, an fitar da sakamakon ne kwanaki 45 bayan kammala takardarw karshe.
Jarrabawar da aka gudanar na tsawon makonni shida daga 16 ga Mayu zuwa 23 ga Yuni, 2022.