An kama wasu da ake zargin sun kai hari cocin St. Francis Catholic Church da ke Owo, jihar Ondo.
Wani faifan bidiyo da ya nuna yadda jama’a ke zanga-zanga a cikin fadar Olowo na Owo, Oba Ajibade Ogunoye.
Ana iya jin daya daga cikinsu yana cewa: “Suna so su kai su Akure. Matasan sun fusata.”
A ranar Lahadin da ta gabata ne wasu ‘yan bindiga suka mamaye cocin tare da kashe wasu masu ibada da suka hada da mata da kananan yara a Ondo.
Jami’an tsaro a ranar Alhamis din nan sun dora alhakin harin kan ‘yan ta’addar Daesh a yammacin Afirka (ISWAP).