Hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta ta nemi goyon bayan rundunar sojojin saman ƙasa, wajen tura ma’aikata da jigilar kayayyakin zabe zuwa wurare masu nisa da rashin tsaro a fadin kasar.
Hukumar ta kuma nemi goyon bayan rundunar sojin sama, domin samar da tsaro a wuraren da ba a taba samun matsala kamar yadda ta saba yi a lokacin zabukan fitar da gwani ba.
A cewar Punch, shugaban hukumar ta INEC, Farfesa Mahmood Yakubu ne ya bayyana hakan a lokacin da ya ziyarci babban hafsan sojin sama, Air Marshal Oladayo Amao a ranar Laraba a Abuja.
“A ranar 25 ga Fabrairu, 2023 da 11 ga Maris, 2023, hukumar za ta tura ma’aikata da kayan aiki zuwa kusan 190,000 wuraren kada kuri’a da tattara kuri’u 1,491 a fadin Najeriya,” in ji shugaban INEC.
Da yake mayar da martani, Amao ya yabawa INEC kan yadda za a inganta harkokin zabe a kasar nan.
Ya yi alkawarin bai wa INEC goyon baya da hadin kai da suka wajaba wajen jigilar dukkan kayayyakin zabe, kayan aiki ciki har da ma’aikatan da ke zuwa Najeriya zuwa kowane yanki na lungu na kowace jiha,domin tabbatar da an gudanar da zabe cikin gaskiya da adalci.