Gwamnan jihar Jigawa, Malam Umar Namadi, ya baiwa ma’aikatan jihar tabbacin shirin gwamnatinsa na aiwatar da sabon mafi karancin albashi da zarar gwamnatin tarayya ta rattaba hannu a kai.
Gwamnan wanda mataimakinsa Aminu Usman ya wakilta a wajen bikin ranar ma’aikata, gwamnan ya taya ma’aikatan murnar wannan rana.
Ya tabbatar da kudirin gwamnatin jihar na tabbatar da biyan albashi da fansho cikin gaggawa a lokacin da ya kamata.
Tun da farko shugaban kungiyar kwadago ta jihar, Kwamared Sanusi Alhassan, kira ya yi da a dauki dimbin ma’aikata da horas da su tare da sake duba kudaden alawus-alawus din da ake ba su, domin nuna halin da ake ciki na tattalin arziki.