Majalisar wakilai ta amince da ayyana dokar ta baci a jihar Ribas duk da adawar da masu ruwa da tsaki suka yi.
Majalisar ta kuma amince da dakatarwar na tsawon watanni shida da aka yi wa Gwamna Siminalayi Fubara, da mataimakinsa, da dukkan zababbun ‘yan majalisar ta hanyar kada kuri’a a ranar Alhamis.