fidelitybank

Da yuwar sasantawa tsakanin Amaechi da Magnus

Date:

Tsohon dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar All Progressives Congress (APC) kuma tsohon ministan sufuri, Rt. Hon. Chibuike Rotimi Amaechi, ya ce, ba shi da masaniya kan duk wani yunkuri da dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu zai yi na sasanta shi da wani jigo a jam’iyyar a jihar Ribas, Sanata Magnus Ngei Abe.

Abe ya taba zama sakataren gwamnatin jihar Ribas a lokacin Amaechi na farko kuma ya wakilci gundumar Ribas ta kudu maso gabas a majalisar dokokin kasa.

Amaechi, wanda ya zanta da manema labarai a sakatariyar jam’iyyar APC ta jihar da ke Fatakwal, babban birnin jihar Ribas a ranar Asabar, ya ce; “Ban san cewa akwai shirin Asiwaju Ahmed Bola Tinubu na sasanta ni da Magnus Abe.”

Tsohon Ministan wanda ya kai ziyararsa ta farko a jihar, tun bayan da Tinubu ya rasa tikitin takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC kimanin makonni hudu da suka gabata, ya ce yana kokarin sasanta duk wasu masu fada a ji a cikin jam’iyyar.

Ya ce: “Duk lokacin da kuka sami canji, tabbas za ku sami sabani. Ina magana ne game da abin dake faruwa a tsakaninmu. A cikin mako ɗaya, biyu, uku, za mu iya warware matsalolin. Batun dan takarar gwamna ba ne. Ina bukatar in zauna da su, in ce, ko za mu iya ci gaba.”

national news today

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

An fara binciken fashewar wani abu da ya kashe mutane 5 da jikkata da dama a Kano

Wani abin fashewa da ake tunanin bom ne ya...

An samu fashewar wani abu a kamfanin ƴan Chana a Kano

An samu fashewar wani abu a Kamfanin Ƙarfe na...

Ma’aikacin kamfani ya kashe abokin aikinsa a Kano

Rahoton da ke yawo a kafafen sada zumunta ya...

Kotu ta ɗaure Matashin da yake tare titi a Kano da sunan barƙwanci

Kotun majistire da ke unguwar Nomansland a Kano, karkashin...

Bayan kashe Soja yanzu haka an kama ƴan Daba 398 a Kaduna

Rundunar 'Yan Sandan Jihar Kaduna, ta sanar da kama...

Shettima zai san makomarsa bayan taron APC na ƙasa – Fadar Shugaban Ƙasa

Fadar shugaban ƙasa ta bayyana cewa, sai bayan babban...

Kotu ta ɗaure Matashin da ya shiga ɗakin kwanan Ɗalibai Mata a Kano

Babbar Kotun Shariʼar Musulunci da ke Kofar Kudu a...

Ban gudu daga PDP ba – Namadi Sambo

Tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Mohammed Namadi Sambo, ya ƙaryata...

Da yuwar Sojojin mu za su shiga yaƙi don tallafa wa Isra’ila – Trump

Rundunar sojin Isra'ila IDF ta ce ta ƙaddamar da...

Isra’ila ta kai hari cibiyoyin ƙera nukiliyar Iran

Yayin da aka shiga rana ta shida na yaƙi...

Najeriya za ta kwashe ƴan ƙasarta dake zaune a Iran da Isra’ila

Gwamnatin tarayya ta ce, tana kammala shirye-shiryen gaggawa domin...

Makami mai Linzami ya faɗa kan cibiyar tattara bayanan sirrin Isra’ila

Kafar yaɗa labarai ta gwamnatin Iran ta ce, ƙasar...
X whatsapp